Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya nuna bacin ransa kan Zanga-zangar makiyaya da manoma

Shugaban kasar Fransa Francois hollande ya nuna bacin ransa dangane da ci gaba da datse hanyoyin mota da makiyaya da manoma ke yi a yankin Lyon.

Shugaban kasar Faransa François Hollande
Shugaban kasar Faransa François Hollande Reuters
Talla

Manoma da makiyaya na daukan wannan mataki ne domin nuna bacin ransu da faduwar darajar albarkatun gonar da suke nomawa a kasar, duk da cewa, gwamnati ta bayyana daukar matakan tallafa masu, da kuma inganta farashin hajojin na su.

Shugaba Hollande ya yi kiran dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar kasuwar kayan gona a kasar, da suka hada da masu Yanka, masu sarrafa kayan gonar da kuma yan kasuwa masu rarrabawa, da su kara bada himma wajen ganin an samu Karin farashi Nama da Madara da faduwar darajarsu ke barazana ga dorewar sha’anin kiwon ga makiyaya da dama a kasar ta fransa.

A dai jiya laraba ne Gwamnatin  Faransa ta bayyana aniyarta na ware Euro miliyan 600 domin tallafawa Manoma da makiyaya da ke fuskanatar matsaloli, al’amarin ya sha haifar da zanga zanga a kasar ta Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.