Isa ga babban shafi
Amurka-Faransa

Hollande ya zanta da Obama kan leken asiri

Shugaban Amurka Barack Obama ya tattauna da takwaransa Francois Hollande na Faransa kan rahoton da shafin Wikileaks ya kwarmato wanda ke zargin Amurka da nadar zantukan shugabannin Faransa tun zamanin Chirac. Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta kira jekadanta na Amurka domin tattauna batun leken asirin da ke neman dagula danganta tsakanin manyan kasashen biyu.

Shugabannin Faransa Jacques Chirac, Nicolas Sarkozy  da François Hollande da Amurka ta nadi zantukansu
Shugabannin Faransa Jacques Chirac, Nicolas Sarkozy da François Hollande da Amurka ta nadi zantukansu REUTERS/Regis Duvignau/Charles Platiau/Stephane Mahe
Talla

Shugaba Obama na Amurka ya yi kokarin wanke kasarsa daga zargin leken asirin shugabannin Turai da shafin wikileaks ya kwarmato.

A tattaunawar da suka yi ta wayar tarho a ranar Laraba, Obama ya jaddada wa takwaransa na Faransa Francois Hollande cewa kasarsa ta daina leken asiri akan shugabannin kasashen Turai.

Wannan kuma na zuwa ne bayan shafin wikileaks ya kawarmato cewa Amurka ta nadi zantukan tsoffin shugabannin Faransa guda biyu Jacques Chirac da Nicolas Sarkozy, da kuma shugaba mai ci na yanzu Francois Hollande.

Al’amarin dai bai yi wa Faransa dadi ba, musamman yadda ta ke kallon Amurka a matsayin aminiyarta.

A cikin sanarwar da ofishin shugaban kasar Faransa ya fitar bayan zantawar shugabannin biyu, Sanarwar tace Obama ya jaddada wa Hollande cewa leken asiri akan aminan juna abun ki ne, kuma tuni suka dakatar da aikin akan shugabannin Turai.

Sai dai kuma mai shafin Wikileaks Julian Assange ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata kasashen Turai su dauki matakin shari’a akan aikin leken asirin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.