Isa ga babban shafi
Faransa

Direbobin Tasi sun yi zanga zanga a birnin Paris

Daruruwan direbobin tasi ne suka gudanar da zanga-zanga tare da kona motoci da kuma toshe tituna da dama a birnin Paris na kasar Faransa domin nuna adawa da wani kamfani moticin tasi mai suna UBER, wanda suke zargi da mamaye kasar.

Gungun masu zanga zangar a birnin Paris.
Gungun masu zanga zangar a birnin Paris. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Masu zanga-zangar da yawansu ya kai dubu 2 da 800 sun fantsama kan titunan birnin na Paris inda daga bisani lamarin ya rikide ya zama tarzoma har da kone-kone tsakanin direbobin tasi na asali da kuma wadanda ke yi wa kamfanin na Uber aiki.

Tun a cikin watan janairun da ya gabata ne aka haramta wa kamfanin na UBER gudanar da ayyukansa a Faransa, to amma duk da haka ya ci gaba da tafiyar da harkokinsa a kasar, lamarin da ya harzuka direbobin tasin.

Firaministan Fransa Manuel Valls wanda ke gudanar da ziyarar aiki a Colombia, ya ce gwamnati za ta gurfanar da masu hannu a tarzomar gaban kotu, kuma ya kara da cewa, ba wanda ya isa ya dauki doka a hannunsa ballantana ma a irin wannan hali na hargitsi da kan iya janyo wa Faransa rasa martabarta a idon duniya musamman ga masu ziyarar Kasar.

A Faransa kawai, kamfanin na UBER mai babbar cibiya a Amurka, yana da fasinjojin da yawansu ya kai dubu 400.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.