Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

'Yan gudun hijira: An gudanar da tarukan gangami a Turai

Dubban Jama’a sun gudanar da tarukan gangami a birane dabam dabam na nahiyar turai a jiya Asabar, inda suka bukaci mahukuntan yankin da su kara kaimi wajan taimakawa baki ‘Yan gudun hijira.

An gudanar da irin wannan gangamin abirnin Landan na Kasar Birtaniya
An gudanar da irin wannan gangamin abirnin Landan na Kasar Birtaniya REUTERS/Kevin Coombs
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa da yiwuwa sama da Mutanen Syria miliyan guda su rasa mahallansu nanda karshen wannan shekarar.

Wani babban jami’in Majalisar a Syria, Yacoub Al-Hillo ya ce, dole ne mahukunta su tashi tsaye domin kawo karshen yake yaken Syria, kuma ya gargadi cewa matukar ba’a magance rikicin ba, to lallai za a ci gaba da samun dubban ‘Yan gudun hijira dake neman mafaka a nahiyar Turai.

To sai dai kuma a yayin da wasu ke nuna goyon bayansu ga ‘Yan gudun hijirar, wasu kuwa basu amince da a ba su mafaka ba.

An dai gudanar da gangamin ne a biranen Landan da Stockholm da Budapest da Madrid.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.