Isa ga babban shafi
Jamus

Tsohon Wazirin Jamus ta Yamma Helmut Schmidt ya rasu

Tsohon wazirin jamus Helmut Schmidt ya rasu yana da shekaru 96 a duniya inda ya bar gadon huldar diflomasiyya mai karfi tsakanin Jamus da manyan kasashen duniya.

Tsohon Wazirin Jamus Helmut Schmidt
Tsohon Wazirin Jamus Helmut Schmidt REUTERS/Fabian Bimmer/Files
Talla

Yanzu haka kasashen duniya na ci gaba da aika sakon ta’aziyyarsu ga kasar ta Jamus, shugaban kasar Fransa Francois Hollande ya danganta rasuwar Schmidt da cewa, daukacin nahiyar Turai ce, ta rasa babban jigo,

Helmut Schmidt ya rasu ne Bayan da a cikin watan agusta aka kwantar da shi a asibiti sakamakon cutar karancin ruwa a jika, inda a cikin watan satumba aka yi masa aikin fidar cire wani daskararen jini ga kafafunsa

tsahon shugaban jam’iyar social-démocrate, da ya zama wazirin Jamus daga 1974 zuwa 1982, na zaune a gidansa dake Hambourg (arewacin kasar Jamus)

Mashayi taba sigari na kin karawa, ya kasance gogaggen masani tattalin arziki da ke tsokaci a mahawarorin siyasa Turai har zuwa ‘yan watannin da suka gabata, inda ya yi tsokaci kan matsalolin tattalin arzikin kasar Girka, da kuma rikicin kasar Ukraine, tare da sukar rashin kwarewar da Angela Merkel kan harakokin tattalin arriziki.

Kimarsa da kuma yadda yake da kaifin basira wajen sharhi kan tattalin arziki sun sa ya kara samun matsayin mutumen da aka fi girmamawa a tsarin siyasar kasar Jamus.

A lokacin bikin cikarsa shekaru 95 a duniya a 2013 binciken ra’ayoyin jama’a da majalar Stern ta gudanar ya nuna cewa shi ne wazirin Jamus da ya fi daraja tun bayan yakin duniya na 2, a gaban takwarorinsa Konrad Adenauer, Willy Brandt da kuma Helmut Kohl.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.