Isa ga babban shafi
Ukraine

An tuna hatsarin nukiliyar Chernobyl a Ukraine

Al’ummar Ukraine sun yi bikin tunawa da hatsarin nukiliyar da ya auku a Chernobyl da ke kasar, wanda ya haddasa hasarar rayukan mutane  yau shekaru 30 da suka gabata. Hatsarin shi ne mafi muni da ya taba aukuwa a duniya.

Tashar nukiliyar Chernobyl a Ukraine
Tashar nukiliyar Chernobyl a Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Tun cikin daren yau ne al’ummar Ukraine suka fara alhinin, na tarwatsewar tashar nukiliya ta Chernobyl.

An buga karaurawa sannan masu jimamin al’amarin sun aza furanni a Chernobyl a daidai misalin karfe 1 da mintina 23 lokacin da tashar nukiliyan ta fashe tare da famtsama zuwa sassan Turai.

Akalla mutane 30 suka mutu a cikin cibiyar ta Chernobyl sannan dubbai aka yi hasashen sun mutu daga tururin nukiliyar da ya tarwatse a tashar wanda aka bayyana mafi muni da ya taba aukuwa a duniya.

An shafe kwanaki 10 wuta na ci a tashar nukiliyar ta Chernobyl.

Har yanzu dai ba’a iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba, saboda rashin samun cikakken bayanai daga bangaren gwamnatin tsohuwar daular Soviet wanda a zamaninta ne al’amarin ya faru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.