Rikici ya mamaye gasar Euro a Faransa
Rikici tsakanin magoya bayan kasashe ya mamaye kanun labaran wasannin gasar cin kofin Turai Euro 2016 da ake gudanarwa a Faransa inda a jiya sai da ‘yan sanda suka tarwatsa magoya bayan kasashen Rasha da Ingila a Lille a bata kashin da suke a saman titi.
Wallafawa ranar:
Akalla mutane 36 ‘Yan Sanda suka kama a Lille. ‘Yan Sandan sun ce mutane 16 aka kwantar a asibiti sakamakon tashin hankali tsakanin magoya bayan Rasha da Slovakia.
Tuni dai Rasha ta kira jekadanta na Faransa domin nuna fushin kame Rashawan da Faransa ke yi a sakamakon rikicin na Euro.
Rasha ta ce kamen ‘yan kasarta ya nuna yadda ake kyamar ta, kodayake Faransa ta ce zata yi adalci wajen hukunta Rashawa da Turawan Birtaniya da aka cafke.
Wasannin Euro 2016
A yau Alhamis kuma ‘Yan Sandan Faransa sun sake damara don fuskantar karawar da za a yi yau tsakanin England da Wales.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu