Isa ga babban shafi
EU- Jamus-Faransa-Italiya

Shugabannin kasashen Jamus, Faransa da Italiya sun ce da Britaniya Allah raka taki gona

Shugabannin kasashen Jamus , Faransa da Italiya sun tsaida shawarar yin iyakacin kokari domin bunkasar kungiyar Tarayyar Turai bayan ficewar kasar Britaniya daga cikin su.  

Shugaban Faransa François Hollande, da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel eda Fira Ministan Italiya Matteo Renzi a taron su a Berlin
Shugaban Faransa François Hollande, da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel eda Fira Ministan Italiya Matteo Renzi a taron su a Berlin John MACDOUGALL / AFP
Talla

Kasashen uku masu karfin fada aji cikin kungiyar ta Tarayyar Turai sun bayyana cewa Britaniya yanzu ya dace ta yi aiki da Doka ta 50 domin sabulewa daga cikin kungiyar, sannan ta tattauna batun harkan cinikayya da sauran hulda da sauran makwabtanta.

Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel mai masaukin baki a tattaunawa da Shugaban Faransa Francois Hollande da Fira Ministan Italiya Matteo Renzi a birnin Berlin ta bayyana cewa sun amince da fitan Britania daga cikin su, amma kuma akwai bukatar  rubutacciyar wasika zuwa ga Hukumar kungiyar Turai domin ta sani.

Ministan Kudi na Britaniya George Osboene tunda fari ya fadi cewa kasar sa za ta bi abinda doka ta 50 ta fadi ne kawai idan har ta hango inda kasar ta dosa da sauran kasashen kungiyar.

Shugaban Gwamnatin Jamus ta fadi cewa babu wani lokaci da za'a bata gameda ficewar, sannan kuma za su duba dacewar matakan da za'a dauka gameda wasu kasashen da suka fara nuna bukatar ficewa daga wannan kungiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.