Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya soma nada mutanen da za su yi aiki tare

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya nada Reince Priebus a matsayin shugaban ma’aikatan fadar White House yayin da Stephen Bannon zai rike mukamin babban mai tsare-tsare da bai wa shugaban shawara kan dabarun mulki.

Stephen Bannon ya shugabanci yakin neman zaben Trump.
Stephen Bannon ya shugabanci yakin neman zaben Trump. REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Stephen Bannon, tsohon shugaban gidan talabijin ne na Breitbart da ya taka muhinmiyyar rawa a yayin yakin neman zaben shugabancin kasar da Mista Trump ya yi nasara.

A daya bangaren kuwa sabon Shugaba Trump ya sha alwashin korar bakin da basu da takardun zama akalla miliyan uku da zarar an rantsar da shi.

Mr Trum ya fadi hakan ne a wata hira da akayi da shi a tashar talabijin din CBS, inda Trump ya ce abinda za suyi shine tattara mutanen dake da tarihin aikata laifufuka da masu hada-hadar kwayoyi akalla miliyan biyu zuwa uku don tusa keyarsu kasashensu na asali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.