Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Julian King ya ce Turai na fuskantar barazanar kutse ta intanet

Babban jami’in kula da sha’anin tsaron Tarayyar Turai Julian King ya ce Nahiyar na fuskantar barazanar kutse ta intanet musamman daga wasu bata-garin da ke neman wargaza hadin kan mambobin kungiyar 28.

Kwamishinan tsaron Kungiyar Tarayyar Turai Julian King
Kwamishinan tsaron Kungiyar Tarayyar Turai Julian King JOHN THYS / AFP
Talla

Mista King ya yi kira ga kasashen Turai su tashi tsaye domin dakile barazanar.

Julian King wanda shi ne kwamishinan tsaron kungiyar Turai ya ce matsalar kutsen ya janyo wa tattalin arzikin Turai asarar kudi kusan miliyan 60 na euro a shekarar da ta gabata kawai.

Kuma ya yi gargadin cewa asarar za ta karu idan har ba a gaggauta daukar matakai ba.

Mista King ya fadi haka ne kafin soma taron tattauna magance matsalar masu kutse ‘yan dandatso da aka soma a jiya a birnin Lille na Faransa.

Amurka dai na zargin Rasha da yi mata kutse a lokacin zaben shugaban kasa, kamar yadda Amurka ta jima tana zargin China da yi mata leken asiri.

Masana a Turai kuma na ganin hakan na iya faruwa a zabukan da za a gudanar a manyan kasashen Turai Faransa da Jamus.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce an samu karuwar matsalar kutsen da kusan kashi 20 a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.