Isa ga babban shafi
Faransa

Jacques Cheminade Dan takarar zaben shugaban Faransa na 2017

Jacques Cheminade na Daya daga cikin yan takara 11 da za su kara da juna a zagayen farko na zaben shugabancin Faransa na 2017 da za a gudanar a ranar 23 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki.

Jacques Cheminade, Dan takarar shugaban kasa a zaben Faransa na 2017
Jacques Cheminade, Dan takarar shugaban kasa a zaben Faransa na 2017 AFP/Joël Saget
Talla

Tarihin Jacques Cheminade

An haifi Jacques Cheminade ne a ranar 20 ga watan Agustan 1946 à Buenos Aires na kasar Argentina.

A 1965 ne ya kammala karatun ilimin shari’a ya kuma karanci ilimin jagoranci da tafiyar da kamfanoni a makarantar da ake kira HEC da kuma ta ENA a 1969 manyan makarantun masu daraja a Faransa.

Ya kasance dan Gurguzu na kin karawa, Jacques Cheminade ya yi aikin gwamnati a ma’aikatar ministan kudi, kafin a nada a matsayin wakilin Faransa kan harakokin kasuwanci a birnin New York na kasar Amurka. Ya kuma bar aikin gwamnati ne a 1981.

A 1982, ya rike mukamin sakataren jam’iyar ‘yan kwadagon Turai (POE) wace a 1991 ta canza suna zuwa jam’iyar (FNS) Fédération pour une nouvelle solidarité.

Tun farkon 1996, ya ke rike da mukamin shugaban jam’iyar yan gurguzu Solidarité et progrès SP

A zaben shekarar 1995 da ya shiga, ya samu 0,27 % na kuri’un da aka kada.

Ya kuma sake tsayawa takara a zaben 2012, sai kuma a wannan karo inda ya sake bayyana sha’awarsa ta sake shiga a fafata da shi a sukuwar neman haye kujerar shugabancin fadar l'Élysée ta shuganacin kasar Faransa a wannan shekara ta 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.