Sojin Isra'ila sun kashe mutane 16 da jikkata sama da 1,400 a Gaza
Kungiyar Kasashen Turai ta bukaci gudanar da bincike mai zaman kan sa kan amfani da karfin da ya wuce kima da Israila tayi a Gaza, wanda yayi sanadiyar kashe Falasdinawa 16.
Wallafawa ranar:
Shugabar diflomasiyar kungiyar Federico Mogherini ta bayyana cewar kungiyar na alhinin kashe mutanen da akayi, kuma suna jajantawa iyalan su da kuma wadanda hadarin ya ritsa da su.
Jami’ar ta ce yancin fadin albarkacin baki da kuma yancin gangami na daga cikin yancin bil Adama da ya dace kowa ya mutunta.
Ma’aikatar lafiyar Gaza ta tabbatar da cewar Israila ta kashe mutane 16 da jikkata sama da 1,400.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu