Isa ga babban shafi
Faransa

Zantawar jagoran Aqmi da tashar talabijin ta France24

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Alqa’ida a yankin Arewacin Afirka Abou Obeida Youssef Al-Annabi, a wata zantawa da tashar talabijin ta France24, ya bayyana matsayin kungiyar dangane da halin da ake ciki a Algeria, da alakar da ke Alqa’ida da IS sai kuma makomar wata Bafaransa mai suna Sophie Petronin da yanzu haka ke hannun barden kunhiyar.

Wani jagoran kungiyar Aqmi a Mali
Wani jagoran kungiyar Aqmi a Mali Video screen grab
Talla

Dan jaridar Fransa24 Wassim Nasr ne ya aika wa Abou Obeida Youssef Al-Annabi wanda ke matsayin shugaban majalisar zartaswa na Alqa’ida a Arewacin Afirka tambayoyi guda 12 a rubuce.

Abou Obeida, wanda tun watan satumbar shekara ta 2015 ne Amurka ta sanya sunansa cikin jerin ‘yan ta’adda na duniya, ya amsa wadannan tambayoyi ta hanyar nadar murya, inda da farko ya jaddada barazana a kan kasar Faransa.

To sai dai jagoran na Aqa’ida ya ce kungiyar a shirye take ta shiga tattaunawa da mahukuntan birnin Paris domin sakin Sophie Petronin, Bafaransar da kungiyar ke ta sace a watan disambar shekara ta 2016 a garin Gao na kasar Mali.

A watan yunin shekarar da ta gabata, an yada wani hoton bidiyo da ke nuna bafaransar a cikin yanayi na gajiya, yayin da wani lokaci a baya, dan wannan mata ya zargin gwamnatin Faransa da kin yin wani katabus domin ‘yantar da mahaifiyarsa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.