Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta tsaurara dokokin hukunta masu cin zarafin yara

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce zai tsaurara dokokin hukunta masu cin zarafin kananan yara ta hanyar lalata dasu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Photo by Ludovic Marin, Pool via AP
Talla

Macron ya sha alwashin ne, jim kadan bayan karanta wani littafi da aka wallafa a Internet, mai dauke da hirarrakin da aka yi da kananan yaran da aka ci zarafinsu, ciki har da wani yaro dake tuhumar wani fitaccen dan siyasa a Faransa da yin lalata da shi.

A shafinsa na Twitter, shugaban na Faransa ya ce tuni ya baiwa ministan shara’ar kasar umarnin fara shirye-shiryen samar da sabbin dokoki masu tsauri da za su baiwa kananan yara kariya.

Wani binciken hukumar lafiya ta duniya WHO ya nuna cewa akalla mace 1 cikin 5 da kuma namiji 1 cikin 13, ke gabatar da korafin an taba cin zarafinsu ta hanyar lalata su a lokacin da suke yara ‘yan kasa da shekaru 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.