Faransa ta killace wasu yankunan kasar 2 saboda korona
Shekara guda bayan killacewar farko da ta haifar da tsayawar Faransa cak, na tsawon watanni 2, a ranar laraba 17 ga watan maris 2021, shugaba Emmanuel Macron ya sake mutunta zabin, mai matukar wahala wajen sake killace yankunan kasar 2, dake fama da matsalar Korona. Yankunan da suka hada da Ile-de-France da Haut-de-France, duk kuwa da alkawalin da ya yi cewa ba zai sake killace yankunan kasar ba.
Wallafawa ranar:
’An toshe ramen Bera a Île-de-France ». wannan Furuci ya fito ne daga bakin daya daga cikin shuwagabanin gungun masu rinjaye a majalisar dokoki a yayin bayyana damuwarsa kan halin matsi da annobar da jefa yankunan a ciki.
Daga cikin niyar da ya dauka, shugaba Emmanuel Macron ya ce zai bi, duk wata hanya da ta dace wajen kaucewa sake killace yankunan kasar, kafin zuwan lokacin da za a yi wa daukacin yankunan alurar rigakafin da zata bada damar kawar da barazanar da ake fuskanta.
Sai dai ‘yan kwanaki bayan haka, yankin birnin Paris mai kunshe da mutane miliyan 12 ya sake fadawa cikin danja, al’amarin da ya tsoratar da wata minista da ta kasa shiga sashen da ke kula da tantance mutanen da suka kamu da korona a Asabiti
A farkon wannan mako ne dai, shugaban Emmanuel Macron ya shanye gajearar kwana a dubu, wajen amincewa kansa cewa ya yi rauni a yaki da annobar da ta gagari duniya, inda ya ce babu shakka ya zama wajibi a sake kara daukar sababin matakai cikin yan kwanaki masu zuwa. Sanarwar umarnin killace yankunan dai ta fito ne daga bakin pm kasar Jean Castex .
A yayin da shi kuma shugaba Emmanuel Macron ya sanya hannun soma aiki da dokar killacewar a ranar laraba 17 ga watan maris 2021.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu