Isa ga babban shafi
Faransa - Gaza

Magoya bayan Falasdinawa na shirin gudanar da zanga-zanga a Faransa

Ministan cikin gidan Faransa Geral Darmanin ya bukaci ‘yan sanda da su haramta  wata zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da ake shirin gudanarwa a karshen mako a Paris kan rikici da take yi da Isra’ila, saboda fargabar sake barkewar tarzoma a irin makamancin wanda aka gani a shekarar 2014.

Karkashin shirin baya ga Falasdinawa milyan 5 da ke cin gajiyar tallafin akwai kuma yaran Falasdinawa kusan dubu dari biyar da 26 da hukumar ta UNRWA ke daukar nauyin karantun a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon da Syria da kuma Jordan.
Karkashin shirin baya ga Falasdinawa milyan 5 da ke cin gajiyar tallafin akwai kuma yaran Falasdinawa kusan dubu dari biyar da 26 da hukumar ta UNRWA ke daukar nauyin karantun a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Lebanon da Syria da kuma Jordan. REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Masu fafutuka sun kira zanga-zangar a gundumar Barbes da ke arewacin Paris don nuna rashin amincewa da yadda Isra’ila ta yi amfani da karfi a Zirin Gaza don mayar da martani ga rokokin da kungiyar Hamas ta harba kan yahudawan.

Ministan cikin gida Gerald Darmanin ya wallafa ta shafinsa na Twitter cewa "ya bukaci shugaban 'yan sanda na Paris da ya hana zanga-zangar na ranar Asabar mai nasaba da rikice-rikicen da ke wakana a Gabas ta Tsakiya."

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin yayi kira ga shugaban 'yan sanda da ya haramta zanga-zanga goyon bayan Falasdinawa

Ya kara da cewa "An ga mummunar hargitsi ga zaman lafiyar jama'a a shekarar 2014," don haka, yana kira ga shugabannin 'yan sanda da ke wasu wurare a Faransa su ma su kula da zanga-zangar.

A watan Yulin 2014 an gudanar da mummunar zanga-zanga da  Faransa don yin Allah wadai da harin Isra’ila kan Zirin Gaza, bayan da sukayi fatali da haramcin da 'yan sanda sukayi, lamarin da ya zama tarzoma tare da jikkata mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.