Isa ga babban shafi
Afrika-Faransa

Macron na karbar bakoncin taron tattalin arzikin Afrika da Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai karbi bakuncin wani taro da zai kunshi shugabannin Turai da na Afrika a ranar Talata, da zummar lalubo mafita a game da matsalar tattalin arziki da ta addabi nahiyar Afrika.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Frederick Florin AFP
Talla

Taron wanda zai tattaaro shugabannin kasashe 30 ta kafar bidiyo, an shirya shi ne a shekarar da ta gabata bayan da asusun lamuni na duniya ya yi kiyasin cewa kasashen Afrika na cikin hatsarin fuskantar gibi na tattalin arziki da ya tasamma dalar Amurka biliyan 290 a shekarar 2023.

Ana sa ran tattalin arzikin nahiyar Afrika wanda ya fuskanci koma-baya a shekarar da ta gabata sakamakon bullar annobar Coronavirus ya farfado da kusan kashi 3 da rabi a wannan shekarar da kuma kashi 4 a shekarar 2022.

Karin wa'adin da kungiyoyin kasashen G20 da na Paris Club suka yi na biyansu rancen da kasashe suka ciyo a watan Afrilun 2020 ya sa Afrika ta samu sa’ida, duba da yadda aka dakatar mata da biyan sama da Yuro biliyan 5.

A watan da ya gabata, shugaba Emmanuel Macron ya yi kashedin cewa kasashe masu ntasowa sun dauko hanyar barin Afrika cikin matsaloli da suka yi musu dabaibayi.

Shugaban na Faransa ya ce daga cikin  hatsarin rashin  daukar mataki a kan halin da tattalin arzikin Afrika ya shiga akwai raguwar damammakin bunkasar tattalin arziki, karuwar ta’addanci da yawaitar kwarara ‘yan nahiyar zuwa kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.