Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Faransa ta sake sassauta dokar takaita walwalar jama'a a sassan kasar

Faransa ta shiga rukuni na 3 a kokarin sassauta dokar takaita walwalar jama’a bayan sake samun raguwar mutanen da ke kamuwa da Covid-19 yau laraba a sassan kasar.

dawowar hada hada a Faransa.
dawowar hada hada a Faransa. © Reuters/Eric Gaillard
Talla

Karkashin matakan da kasar ta Turai ke bi, daga yau za ta sahale bude wasu kasuwanci da hada-hadar jama’a a yankunan da ke fuskantar dokokin takaita walwalar tsawon watanni.

Haka zalika daga yau laraba Faransar za ta janye dokar hana yawon dare baya ga baiwa gidajen abinci da wuraren shakatawa damar ci gaba da budewa bayan kasancewarsu a kulle tsawon watanni 7.

Kafin yanzu dai gidajen abinci na da damar iya sayarwa da mutane ne kadai ba tare da basu damar zaunawa a harabarsu ba, haka zalika gidajen abinci da sauran wuraren cinikayya.

Sai dai karkashin matakan wanda suka janye dokar hana fita sun sahale baiwa mutane 6 damar zama a teburin abinci guda haka zalika bangaren barasa amma bisa sharadin bayar da cikakkiyar tazara tsakanin jama’a.

A bangare guda Faransar ta jaddada haramcin yawo ba tare da takunkumin fuska ba, haka zalika haduwar mutane fiye da 10 a waje guda ba tare da tazara ba, har zuwa nan da 30 ga watan nan don sanar da mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.