Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Faransa ta janye dokokin takaita walwala duk da barazanar covid-19

Faransa ta kammala janye dokokin takaita walwalar da ta sanya kan gidajen abinci da na sinima baya ga guraren shakatawa da kuma shagunan sayayya a kokarin dakile yaduwar covid-19, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da kasar ke sake ganin barkewar cutar a karo na 4, ko da ya ke wasu yankunan sun gamu da sabbin dokoki.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Duk da matakin janye ilahirin dokokin takaita walwalar a yau Laraba, yankin kudancin Faransa na ci gaba da fuskantar tsauraran matakan yaki da cutar bayan yaduwar nau’in coronavirus ta Delta wadda ke matsayin barkewar cutar karo na 4 da kasar ta Turai ke gani.

Tuni dai likitan da ke jagorancin kwamitin yaki da covid-19 na Faransar Dr Jean-Francois Delfraissy ya gargadi shugaba Emmanuel Macron kan hadarin da matakin ke da shi bayan hasashen yiwuwar barkewar cutar a karo na 4 da za a gani musamman nau’in Delta da ke ci gaba da barna a kudancin kasar.

A cewar likitan nau’in Delta da Faransar za ta gani ba za ta kai hadarin 3 da kasar ta gani a baya ba, sai dai ba lallai rigakafin da ake amfani da shi yanzu haka ya iya yiwa jama’a aiki ba, la’akari da yadda aka samar da rigakafin don nau’in da suka gabata.

A wata tattaunawarsa da gidan radiyon Inter da ke Faransar, Delfraissy ya ce har zuwa yanzu kashi 1 bisa 3 na al’ummar kasar ne suka karbi rigakafin cutar wanda ke nuna akwai bukatar sanya tsauraran matakai don hana yaduwar nau’in Delta wadda ta fi barazana ga matasa da masu karancin shekaru.

Faransar wadda zuwa yanzu ta rasa jumullar mutum dubu 111 da 86 tun bayan barkewar cutar zuwa yanzu na shirin karkare janye sauran dokokin takaita walwalar jama’ar a ranar 9 ga watan yuli, yayinda ta ke ci gaba da samun raguwar sabbin kamuwa da cutar a kowacce rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.