Isa ga babban shafi

Kungiyar Turai na taro da kungiyar NATO a Lituania

Mahakuntan kungiyar tarayyar Turai da na kungiyar tsaro ta Nato a yau lahadi a kasar Lituania domin tattauna matsalolin yan ci ranin kasar Belarus da kuma na karin girke sojojin Rasha kan iyakar kasar Ukraine.

Cibiyar tsaro ta NATO
Cibiyar tsaro ta NATO © Yves Herman/REUTERS
Talla

Babban sakataren kungiyar tsaro ta Nato, Jens Stoltenberg, ya sake jaddada kira ga mahukumtan Mosco na  Rasha dake jibge sojojinta kan iyakar kasar ukrain da cewa ta yi hattara a kan irin sakamakon da zata girba idan ta ce zata yi amfani da karfi.

Rundunar tsaron Rasha
Rundunar tsaron Rasha © Russian Defense Ministry Press Service via AP, File

Wannan ziyara da  Stoltenberg da shugabar kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Turai, uwargida  Ursula von der Leyen suka kai a  kasar Lituania, ta zo ne kafin zuwan taron da ministocin harakokin wajen kungiyar tsaro ta Nato a gobe talata da jibi laraba, zaman taron da sakataren harakokin wajen Amruka Antony Blinken zai halarta, zai tabo damuwar da ake da ita a yankin kan iyakar da ta hada rasha da ukrain.

Sakatary NATO General Jens Stoltenberg
Sakatary NATO General Jens Stoltenberg REUTERS - GLEB GARANICH

M. Stoltenberg da uwargida von der Leyen dukkaninsu sun zargi kasar Bélarus da haddasa rikicin yan ci rani da ya jawo wa tarayyar turai barazana ta ko wane fanni, zargin da mahukumtan Minsk suka musanta.

 

A yan watanni da suka gabata dubban mutane ne dai, mafi yawa  yan asalin gabas ta tsakkiya suka tsallaka, ko kuma yinkurin ketarwa a cikin kasar Belarus, domin isa kasashen yankin turi ta gabas mambobin kungiyar tarayyar turai da Nato, kasashen da suka hada da Lettonie, Lituanie da kuma Pologne. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.