Isa ga babban shafi
Jamus

Dan bindiga ya kai hari kan jami'a mafi tsufa a Jamus

Wani dan bindiga ya kai hari a dakin karatu na jami’ar Heidelberg da ke kudu maso yammacin Jamus a jiya Litinin, inda ya kashe wata budurwa tare da raunata wasu mutum uku kafin daga bisani ya arce daga wurin.

'Yan sanda da jami'an kashe gobara a harabar jami'ar Heidelberg, bayan da wani dan bindiga shi kadai ya raunata wasu da dama a wani hari da ya kai kan wani dakin karatu, kafin ya harbe kansa har lahira a Heidelberg, Jamus, 24 ga Janairu, 2022.
'Yan sanda da jami'an kashe gobara a harabar jami'ar Heidelberg, bayan da wani dan bindiga shi kadai ya raunata wasu da dama a wani hari da ya kai kan wani dakin karatu, kafin ya harbe kansa har lahira a Heidelberg, Jamus, 24 ga Janairu, 2022. REUTERS - TILMAN BLASSHOFER
Talla

Bayanai daga hukumomin kasar sun ce, daga bisani dan bindigar ya kashe kansa, bayan da ya yi harbin kan mai uwa dawabi a kusa da dakin karatun na ‘Amphitheater’.

Kafofin yada labaran Jamus sun ruwaito cewa harin bashi da wata manufa ta addini ko siyasa.

Rahotanni sun kara da cewa dukkanin mutanen hudun da abin ya shafa sun samu mummunan rauni, guda daga cikinsu kuma ta mutu a asibiti.

Harbin dai ya haifar da firgici sosai, wanda tuni jami’an tsaro suka shiga jami’ar cikin kankanin lokaci, inda 'yan sanda a shafin Twitter suka bukaci jama'a da su kaucewa wurin domin ma'aikatan ceto da na agaji su gudanar da aiki cikin sauki.

'Yan sanda sun baza karnuka a harabar jami'ar, kuma an ga masu bincike suna duban wata bindiga da ke ajiye a kasa.

Jami'ar Heidelberg, wacce aka kafa a cikin 1386, ita ce jami'a mafi tsufa a Jamus kuma guda daga cikin jami’o’I mafiya shahara a nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.