Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta kirkiro fasahar gane fuskokin 'yan ta'adda

Gwamnatin Jamus, zata fara gwajin wata fasahar zamani, da masananta suka kirkira don tantancewa, tare da tona asirin mutanen da ake nema ruwa a jallo, bisa zargin alaka da ta’addanci.

Jamus zata fara amfani da fasahar tantance fuskokin 'yan ta'adda a tashar jiragen ruwa
Jamus zata fara amfani da fasahar tantance fuskokin 'yan ta'adda a tashar jiragen ruwa
Talla

Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere, ya ce, fasahar, wadda zata rika tantance fuskokin wadanda ake nema ruwa a jallo, za’a fara gwajinta a babbar tashar jirgin kasa, da ke birnin Berlin, idan kuma aka samu nasarar gwajin, za’a fadada fara amfani da fasahar a sauran tashohin jiragen kasa da sassan kasar.

A shekarar 2016 da ta gabata wani dan kasar Tunisia yayi amfani da babbar mota wajen bi takan mutanen da ke cin kasuwar Kirsimeti a Berlin inda ya kashe mutane 12.

A waccan lokacin mai laifin ya samu nasarar tserewa ta hanyar bin jirgin kasa, inda ya samu nasarar ketara iyakoki ba tare da an kama shi ba, sai daga bisani jami’an yan sanda suka harbe shi a tashar jirgin kasa da ke birnin Milan na kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.