Isa ga babban shafi
Faransa

An samu raguwar marasa aikin yi a Faransa irinsa na farko a shekaru 10

Faransa ta sanar da samun raguwar marasa aikin yi a sassan kasar mafi karanci cikin kusan shekaru 10, wanda ke nuna yadda kasar ke farfadowa daga mummunar illar da coronavirus ta yi mata a baya-bayan nan.

Shugaba Emmanuel Macron da ke fatan sake tsayawa takara a zaben kasar na watan Aprilu.
Shugaba Emmanuel Macron da ke fatan sake tsayawa takara a zaben kasar na watan Aprilu. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Wasu alkaluma da Ma’aikatar kwadago ta Faransa ta fitar ta ce kididdigar marasa aikin ya sauka zuwa kashi 12 da digo 6 wanda ke matsayin mafi karanta da kasar ta gani tun bayan shekarar 2012.

Alkaluman sun nuna yadda adadin marasa aikin a watannin Oktoba zuwa Disamban 2021 ya kai miliyan 3 da dubu 300 a sassan kasar wanda ke nuna matukar raguwarsu idan an kwatanta da makamancin lokacin a shekarar 2020.

Ministar kwadago ta Faransar Elizabeth Borne cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce shekarar 2021 shekara ce ta aikin yi haka zalika shekarar da muke ciki, da nufin warware matsalar da kasar ta samu kanta a ciki sakamakon ta’azzarar annobar corona.

Haka zalika wani babban masanin tattalin arziki na ma’aikatar Philippe Waechter ya ce alamu sun nuna yadda ma’aikatu kamfanoni da kuma masana’antu ke shirye wajen daukar sabbin ma’aikata a kokarin da kasar ke yi na ficewa daga matsalar tattalin arzikin da annobar corona ta haifar mata.

Dai dai lokacin da Faransar ke tunkarar zaben shugaban kasa a watan Aprilu cike da fargabar hauhawar farashin kayaki ministar ta kwadago ta  ce manuofinsu na samar da ayyukan yi, na samun gagarumar nasara don ragewa jama’a radadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.