Isa ga babban shafi
Faransa - Ukraine

Faransa za ta aike da kayan aikin soji da fetur ga Ukraine

Fadar shugabancin Faransa ta ce gwamnatin kasar za ta aike da karin kayan aikin soji, da kuma man fetur zuwa Ukraine, domin taimakawa wajen yaki da mamayar da Rasha ta yi mata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. © AFP
Talla

Sanarwar ta kuma ce Faransar za ta laftawa Rasha karin takunkuman karya tattalin arziki.

A cewar Fadar Elysee, sabbin takunkumin za su kunshi "matakan kwace kadarori da kuma kudaden manyan jami’an gwamnatin Rasha.

Ministocin harkokin wajen na kungiyar tarayyar Turai EU za su gudanar da taro a yau Lahadi kan bukatar amsa kiran Ukraine na karfafa ba ta tallafin soji da kuma tsaurara takunkumi kan Rasha dangane da afka matan da ta yi da yaki.

Tattaunawar gaggawar ya zo ne jim kadan bayan da Jamus ta janye adawar ta na hana Rasha amfani da tsarin bai daya tsakanin kasa da kasa na hada-hadar sadarwar bankunansu da ake kira da SWIFT, daya aga cikin manyan bukatun kasar Ukraine.

Zalika Jamus ta kuma amince da baiwa Ukraine tallafin makamai, abinda ke nufin ta sauya manufar da ta dade tana amfani da ita, na haramta fitar da makamai zuwa yankunan da ake rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.