Isa ga babban shafi
Faransa-Ukraine

Zai dauki tsawon lokaci kafin kawo karshen yakin Rasha a Ukraine- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine zai dauki dogon lokaci sakamakon yadda al’amura ke tafiya.

Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban taron EU da ke tattaunawa kan rikicin Rasha da Ukraine.
Shugaba Emmanuel Macron yayin jawabinsa gaban taron EU da ke tattaunawa kan rikicin Rasha da Ukraine. REUTERS - POOL
Talla

Yayin da ya ke tsokaci akan halin da ake ciki a Ukraine, Macron ya ce yakin zai dauki dogon lokaci kafin aga bayan sa, saboda haka ya dace duniya ta shirya fuskantar matsalolin da yakin zai haifar.

Macron ya shaidawa taron bikin nuna amfanin gona cewar ya dace jama’ar kasar su shirya tinkarar matsalar da zata biyo baya.

Shugaban na Faransa ya katse halartar bikin baje-kolin amfanin gonar wajen komawa fadarsa domin tinkarar rikicin dake gudana a Ukraine.

Macron ya ce yaki ya koma nahiyar Turai, kuma shugaban Rasha Vladimir Putin ne ya haifar da shi akan mutanen Ukraine wadanda da ke bijirewa kasar sa da kuma rungumar kasashen Turai.

Shugaban ya sake kiran wani taron majalisar ministocin sa da na tsaro na gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a Ukraine.

Takunkumin da aka kakabawa Rasha sakamakon wannan yakin zai yi matukar illa ga bangaren cinikin barasar da Faransa ke sarrafawa, yayin da shugaba Macron ke Nazari akan yadda za’a taimakawa bangaren.

Shugaba Macron ya taka rawa sosai wajen hana barkewar yakin ta hanyar diflomasiya, inda ya dinga kai gwauro yana kai mari tsakanin shugabannin Rasha da Ukraine da Jamus da kuma Amurka domin ganin an kaucewa tashin hankalin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.