Macron ya tattauana da Putin da Zelensky kan shirin mamayar Rasha
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa na Rasha Vladimir Putin da na Ukraine Volodymyr Zelensky a wanna Lahadi a wani yunkuri na karshe da yake yi na dakile shirin Moscow na mamaye Ukraine.
Wallafawa ranar:
Fadar gwamnatin Faransa ta Elysee tace, Macron ya fara tataunawar tsawon mintuna 105 da shugaban Putin, wanda ke zuwa makonni biyu bayan da ziyarar da ya kai birnin Moscow domin lallashin Putin da ya hakura da tura dakaru a kan iyakar Ukraine.
Haka zalika tattauanawar ta yau na zuwa ne, kwana guda bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya shaidawa Macron cewa ba zai mayar da martani ga abin da ya kira tsokanar Rasha ba.
Bayan tattaunawa da Putin a wannan Lahadi, Macron ya ci gaba da tattaunawa da Zelensky ta wayar tarho, in ji fadar shugaban Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu