Ana ta caccakar Rasha a kan harin tashar nukiliyar Ukraine
Ukraine da kawayenta sun bayyana bacin ransu bayan da Rasha ta yi luguden wuta a kan tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya mafi girma a nahiyar Turai, a yayin da take ci gaba da kai hare hare a manyan biranen Ukraine.
Wallafawa ranar:
Sai dai da alama tashoshin samar da wutar lantarki na nukiliya guda 6 dake birnin Zaporizhzhia ba su lalace ba, duk da gobarar da ta tashi a cikinsu sakamakon hare haren.
Amma Ukraine ta zargi Rasha da ta’addanci mai nasaba da nukiliya, a yayin da manzon Amurka a majalisar dinkin duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce harin na kunshe da hatsari tare da halin ko-in-kula.
Rasha ta musanta zargin cewa ta yi luguden wuta a kan tashoshin nukliya.
A cewar Ukraine, dubban fararen hula ne suka mutu, tun da shugaban Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da mamaya a kan kasar a ranar 24 ga watan Fabrairu, sakamakon ikirarin da yake na yaki da barazanar yammacin Turai a kan iyakar kasarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu