Isa ga babban shafi
NATO-Rasha-Ukraine

NATO ta ce yakin Rasha da Ukraine ba nata ba ne

Babban sakataren kungiyar tsaro ta  NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine ba, biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.

Babban Sakataren NATO  Jens Stoltenberg.
Babban Sakataren NATO Jens Stoltenberg. REUTERS - YVES HERMAN
Talla

A yayin wani  taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kasashen NATO, Stoltenberg ya ce  hanya daya tilo da za  a bi wajen aiwatar da dokar hana zirga zirgar jiragen sama a Ukraine ita ce ta harbo jiragen saman Rasha, kuma yin haka zai kai ga babban yaki a Turai, wanda zai shafi kasashe da dama.

Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a  kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba da hare hare a fadin kasar.

NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane,  ta dau wannan mataki ne duk da magiyar da  shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen  kasarsa.

Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.