Isa ga babban shafi
Rikicin Ukraine

Rasha ta laftawa shugaban Amurka da wasu manyan jami'ansa takunkumi

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da haramtawa shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami'ansa goma sha biyu shiga kasar, a wani mataki na mayar da martani ga takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta laftawa Rashan.

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Rasha Vladimir Putin. AFP - MANDEL NGAN,MIKHAIL METZEL
Talla

Daga cikin manyan jami’an Amurkan da Rasha ta haramtawa shiga cikinta, har da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sakataren tsaro Lloyd Austin.

Har ila yau Rasha ta saka sunayen shugaban hafsan hafsoshin sojan Amurka Mark Milley da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan da daraktan hukumar leken asiri ta tsakiya William Burns da kuma sakatariyar yada labaran fadar White House Jen Psaki cikin bakin kundinta.

A makon da ya gabata, Amurka ta haramtawa shugaban Rasha Vladimir Putin da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov shiga cikinta, bayan laftawa gwamnatin kasar ta Rasha takunkumin karya tattalin arziki, matakin da ya samu goyon bayan manyan kasashen yammacin Turai, saboda yakin da ta kaddamar kan Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.