Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Harin Sojin saman Ukraine zai kawo tsaiko a tattaunawarmu- Rasha

Rasha ta yi ikirarin cewa harin da jirgin yakin Ukraine ya kai mata ka iya haddasa nakasu a tattaunawar bangarorin biyu da ke kokarin kawo karshen yakin da suke da juna na fiye da wata guda.

Wannan ne karon farko da Ukraine ke kaddamar da hari kan kasar Rasha.
Wannan ne karon farko da Ukraine ke kaddamar da hari kan kasar Rasha. AFP PHOTO / GREG BAKER
Talla

Dai dai lokacin da bangarorin biyu ke ci gaba da tattaunawa da juna, kwatsam jirgin yakin sojin Ukraine ya kaddamar da farmaki kan depon man fetir din Rashan da ke garin Belgorod, lamarin da ya fusata mahukuntan Moscow yayin da fargaba ta karu kan yiwuwar rikicin kasashen biyu ya tsananta.

Yau juma’a dai aka koma tattaunawa ta bidiyo tsakanin wakilan bangarorin biyu, sai dai mahukuntan Rasha sun yi gargadi kan yiwuwar ruruwar yakin sakamako farmaki kan kasarsu, duk da alwashin da suka dauka na tsagaita hare-hare tare da janye dakaru daga wasu yankuna na birane Kiev da Chernigiv.

Sai dai a bangare guda bayan farmakin Sojin na Ukraine karon farko a cikin Rasha, shugaba Volodymyr Zelensky ya yi ikirarin cewa sun dauki matakin ne saboda bayanan da suke samu na cewa, Rash ana shirin kaddamar da wasu mugayen hare-hare a yankunan gabashi da kudancin kasarm, yana mai cewa janyewar da dakarun ke yi ba wai yunkuri ne na tsagaita wuta ba, said ai shirin sake dunkulewa don afkawa wani yanki na Ukraine.

A jawabin Zelensky na cikin daren jiya, shugaban ya ce janyewar ta Rasha daga Kiev wani sabon salon dabarun yaki ne da kasar ke amfani da shi don karkatawa daga inda Sojojinta ke shan wahala zuwa yanki da suka san lallai zai wahalar da Sojin Ukraine a gwabza yaki.

Shugaba Zelensky ya bayyana cewa Sojin Rasha sun tsananta hare-hare kan yankunan Donbas da Mariupol dukkaninsu a Kharkiv dai dai lokacin da Amurka ke gargadin cewa matakin zai tsananta yakin fiye da hasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.