Isa ga babban shafi

Macron ya yi wa yeriman Saudiyya kakkayawar tarba a ziyarar da ya kai Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tarbi Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman da ake kira (MBS) inda suka yi musabaha da ta dauki hankali a fadar Elysée da ke birnin Paris, a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fusata kan ganawar tasu.

Yeriman Saudiyya mai jiran gado,  Mohammed ben yayin musabaha da Emmanuel Macron, na Faransa a Paris.
Yeriman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed ben yayin musabaha da Emmanuel Macron, na Faransa a Paris. AFP - BERTRAND GUAY
Talla

MBS, sanye da rigar gargajiya ta Saudiyya, sun yi doguwar musabaha da Macron, kafin suka garzaya cikin Fadar Elysée.

Babu wani mutum da ya yi wani sharhi amma ana sa ran sanarwa daga baya daga Elysée bayan tattaunawar.

Wani jami'in fadar shugaban kasar Faransa ya shaida wa manema labarai cewa Macron zai gabatar wa bakon nasa tambayoyin kan kare hakkin bil'adama, ciki har da shari'o'in daidaikun mutane, da kuma tattauna batun hako mai da yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Wannan na zuwa ne bayan ganawar da shugaban Amurka Joe Biden yayi da MBS a farkon wannan watan a matsayin wata alama ta sake janyo yarima mai jiran gadon saudiyar  cikin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.