Isa ga babban shafi

Mun tattauna batun kisan Khashoggi da Yarima bin Salman na Saudiya - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya tabo batun kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 2018 "a ganawar da ya yi ranar Jumma’a da Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman da ake kira (MBS) a Jeddah, a rana ta uku na rangadinsa na farko a Gabas ta Tsakiya a matsayinsa na shugaban kasa.

Shugaban Amurka Joe Biden da Yarima bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiya a birnin Jedda, 15/07/22.
Shugaban Amurka Joe Biden da Yarima bin Salman mai jiran gadon sarautar Saudiya a birnin Jedda, 15/07/22. © Bandar Aljaloud/AP
Talla

Mista Biden yace "Abin da ya faru da Khashoggi ya yi matukar tayar da hankali...kuma ya bayyana karara, idan wani abu makamaicin haka ya sake faruwa, to zasu maida martani.

Biden yace batun da ya fara tattaunawa da MBS, kenan tun ma kafin zantawarsu ta yi nisa da mutumin da  jami'an leken asirin Amurka suka yi imanin shi ya ba da umarnin kisan gillar da akayiwa Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiya dake Turkiya.

Ziyar da Biden ya kai kasar Saudiyya tare da ganawa da Yarima Ben Salman, ta yi hannun riga da alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zaben shugaban kasa,  na mai da masarautar saniyar ware saboda take hakkin dan Adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.