Isa ga babban shafi

Amurka ta yaba wa Saudiya kan dage haramcin shawagin jiragen Isra'ila a yankinta

Saudi Arabia ta sanar a yau Juma’a cewa, za ta janye duk wata dokar haramta wa wasu jirage ratsa sararin samaniyarta, abin da ke alamta aniyarta ta sasanta wa da Isra’ila gabanin ziyarar shugaban Amurka Joe Biden.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Tuni shugaban na Amurka ya jinjina wa Saudiya game da wannan mataki da ta dauka mai cike da tarihi kamar yadda wata sanarwar fadar White ta ce.

Ana ganin matakin bude sararin samaniyar zai samar da kafar kulla alaka da Saudiya da wasu kasashen Larabawa, abin da Isra’ilar ta dade tana nema.

A cikin sanarwar,mai ba wa shugaban amurka shawara a fannin tsaro, Jake Sullivan ya ce wannan ci gaba da aka samu, sakamako ne na jajjircewa da kuma riko da akidar diflomasiyya da shugaba Joe Biden ya yi.

Ya ce Biden zai sauka kasar Saudiyya a Juma’ar nan, inda zai fadada jawabi a game da ci gaban da aka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.