Isa ga babban shafi

Ukraine ta gano kaburbura 450 a Izyum bayan kwato yankin daga hannun Rasha

Ukraine ta sanar da gano wasu sabbin kaburbura manya har 450 a birnin Izyum na gabashin kasar bayan da dakarunta suka ci gaba da samu gagarumar nasarar ta fuskar kwace manyan birane daga hannun Sojin Rasha.

Wani yanki da aka gano tarin kaburbura a Izyum na gabashin Ukraine.
Wani yanki da aka gano tarin kaburbura a Izyum na gabashin Ukraine. AP - Evgeniy Maloletka
Talla

Hadiman fadar shugaban Ukraine, Mykhaylo Podolyak tarin kaburburan guda ne cikin cikin manyan-manyan kaburburan da suka gano a yankin na Izyum da ya shafe tsawon watanni a hannun dakarun Rasha, wadanda suka rika azabatar da mutanen yankin da kuma yi musu kisan gilla.

Wasu hotuna da Podolyak ya wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka gano tarin gawarwakin jama’a makare a cikin kaburburan, inda a kasa ya yi rubutun cewa ta’addanci da kama karya baya ga take hakkin dan adam ya hallaka tarin fararen hula.

Sanarwar alkaluman kaburburan a yau juma’a na zuwa ne bayan tun a daren jiya shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana gano kaburburan amma ba tare da sanar da adadi ko kuma yawan mutanen da ke kunshe a ciki ba.

Dukkanin sanarwar da Ukraine ta fitar game da gano kaburburan bata bayyana ko dukkaninsu fararen hula ne ko kuma jami’an tsaro ba, haka zalika kai tsaye bata bayyana dalilin mutuwarsu ba.

Akwai dai zarge-zarge da ke alakanta Rasha da aikata laifukan yaki a wasu daga cikin biranen Ukraine ciki har da garuruwan da ke gab da Kyiv fadar gwamnatin kasar.

Tun cikin watan Maris aka sanar da gano wani makeken kabari dauke da tarin fararen hula wadanda gwaje-gwaje suka tabbatar da cewa sai da suka sha bakar azaba gabanin mutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.