Isa ga babban shafi

Ukraine ta sake kwato wasu yankunanta daga hannun Rasha

Ukraine, ta ce dakarunta sun yi nasarar kwace yankuna da dama daga hannun dakarun kasar Rasha, musamman a yankin gabashi da kudancin kasar, a daidai lokacin da Rashar ke cewa ta janye dakarunta daga yankin ne a matsayin dubarun yaki.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. AP
Talla

Janar Valeri Zaloujn, babban kwamandan tsara dubarun yaki na rundunar sojin Ukraine, ya ce kawo yanzu, sun yi nasarar sake kwace yankunan da fadinsu ya kai murabba’in kilomita dubu uku daga hannun dakarun  na Rasha, yana mai cewa duka duka tazarar da ke tsakaninsu da iyakar Rasha bai wuce kilomita 50 ba.

A rana 2 ga watan yunin da ya tabata, shugaba Volodymyr Zelensky, ya ce 20% na kasar wadda ya kai fadin murabbi’in kilomita dubu 125 na karkashin mamayar Rasha ne, ciki har da Crimea da kuma Donbass.

A farkon wannan wata ne dakarun Ukraine sun sanar da kaddamar da gagarumin farmaki da nufi sake kwato kasar daga mamayar Rasha, yayin da a farkon makon jiya Ukraine ta yi nasarar kwato wasu garuruwa da ke lardin Kharkiv da suka jima karkashin mamayar dakarun Moscow. Duk da cewa da farko ana nuna shakku a game da ikirarin nasara da Ukraine ke bayyanawa, amma sanarwar da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar a ranar asabar da ta gabata, ta tabbatar da janyewar dakarun kasar daga Balakliia, da Izioum da ke kusa da birnin Donesk a kudancin kasar Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.