Isa ga babban shafi

Gobara ta hallaka mutane 10 a kusa da Lyon na kasar Faransa

Akalla mutane 10 suka gamu da ajalisu a kusa da birnin Lyon na kasar Faransa ciki harda kananan yara biyar masu shekaru 3 zuwa 15 sakamakon wata gobara ta tashi a a wani gini da ke Vaulx-en-Velin.

Masu aikin kashe Gobara na kasar Faransa a inda aka samu gobra a Vaulx-en-Velin dake kusa da birinin Lyon,16/12/22.
Masu aikin kashe Gobara na kasar Faransa a inda aka samu gobra a Vaulx-en-Velin dake kusa da birinin Lyon,16/12/22. AFP - OLIVIER CHASSIGNOLE
Talla

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Gerald Darmanin wanda ya sanar da lamarin ya ce ba a san musabbabin abin da ya haifar da gobarar ta wannan Jumma’a ba a halin yanzu, amma ana gudanar da bincike kamar yadda ya tattauna da shugaban kasar Emmual Macron.

Yace an aike kimanin jami’an kashe gobara 180 zuwa ginin mai hawa bakwai, kuma sunyi nasarar kasheta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.