Isa ga babban shafi

Sojojin Ukraine sun kakkabo jiragen Rasha marasa matuka 45

Rundunar sojin saman Ukraine ta ce ta samu nasarar kakkabo jirage marasa matuka 45 daga cikin tarin makaman masu linzami da Rasha ta yi amfani da su wajen kai hare-hare a birnin Kyiv da wasu biranen kasar a cikin daren ranar Asabar.

Wasu 'Yan Sandan  Ukraine yayin kokarin harbo jirage marasa matuka da Rasha ke amfani da su wajen kai musu hare-hare.
Wasu 'Yan Sandan Ukraine yayin kokarin harbo jirage marasa matuka da Rasha ke amfani da su wajen kai musu hare-hare. © REUTERS/Vadim Sarakhan/File Photo
Talla

Kamar a lokutan baya ma dai, rundunar sojin ta Ukraine ta ce makamai masu linzamin da ta kakkabo kirar Iran ne, kasar da kasashen yammacin Turai suke zargi da taimaka wa Rasha a yakin da ta kadddamar kan makwafciyar ta ta.

Sanarwar ta ce an harbo jiragen marasa matuka 13 a cikin daren karshen shekarar 2022 da kuma wasu 32 a cikin sabuwar shekara ta 2023. Sai dai mahukuntan na Ukraine ba su bayyana ko wasu daga cikin jiragen marasa matuka sun samu nasarar kai harin da aka nufa.

An kai hare-haren ne a daidai lokacin da aka shiga watanni 11 da barkewar yaki tsakanin Rasha da Ukraine, bayan umarnin kaddamar da mamayar da shugaba Vladimir Putin ya bayar a ranar 24 ga watan Fabarairun shekarar 2022.

Bayan fuskantar koma baya a yakin da suka kaddamar, daga bisani sojojin Rasha sun rika kai hare hare kan ababen more ciki har da cibiyoyin samar da wutar lantarki, lamarin da ya bar miliyoyin mutane cikin sanyi da duhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.