Isa ga babban shafi

Kasashen Turai sun cimma matsaya kan tsaurara dokokin tisa keyar bakin haure

Ministocin kula da harkokin cikin gida na kasashen Turai sun cimma matsaya inda suka yi barazanar tsaurara matakan samun takardun izinin shiga kasashen su ga duk wata kasa da ta ki kwashe ‘yan gudun hijirar ta da ke nahiyar. 

Wasu bakin haure da ke neman mafaka a Budapest.
Wasu bakin haure da ke neman mafaka a Budapest. Reuters/Laszlo Balogh
Talla

Minister kula da harkokin cikin gidan Sweden Maria Malmer Stenegard da ta karbi bakuncin taron da suka gudanar ne ta bayyanawa taron manema labarai matsayar ta su. 

Ministocin sun amince ayi amfani da matakan da suka cimma a shekarar 2020 wajen abinda ya shafi mayar da baki masu neman mafaka da ba su samu matsugunni ba kasashen su na asali. 

Ministar kula da harkokin cikin gida na kungiyar tarayyar Turai Ylva Johansson ta ce kasashen nahiyar da dama na fuskantar matsin lammba ganin yadda a shekarar da ta gabata sun amshi bukatar kusan mutane miliyan daya da ke neman mafaka a cikin su. 

A cewar ta nahiyar a yanzu ba ta da karfin kula da ‘yan gudun hijirar, ganin yadda akwai kusan mutane miliyan hudu ‘yan kasar Ukraine da ke gudun hijira a cikin su saboda mamayar da Rasha ta yi a kasar. 

Ta ce akwai bukatar kara yawan adadin ‘yan gudun hijirar da ake mayarwa kasashen su na asali. 

A karkashin sabuwar dokar masu neman mafaka a nahiyar Turai, kowa za’a ji dalilan da suka shi ya baro kasar sa mai makon yi musu kudin goro. 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.