Isa ga babban shafi

Gidajen yarin Faransa na fama da cunkoson fursunoni

Alkaluma sun bayyana cewa gidajen yarin Faransa na makare da adadin fursunonin da ya wuce kima a fadin kasar.

Sai wata kotu da ke bincike kan yadda gwamnati ke kashe kudade ta gano a wani rahoton baya-bayan cewa Faransa na tafiyar hawainiya wurin magance matsalar cunkoson gidajen yarin.
Sai wata kotu da ke bincike kan yadda gwamnati ke kashe kudade ta gano a wani rahoton baya-bayan cewa Faransa na tafiyar hawainiya wurin magance matsalar cunkoson gidajen yarin. AP - Christophe Ena
Talla

Sakamakon kidayar da aka yi a ranar daya ga watan Afirilu ya nuna fursunoni dubu 73,080 ne ke daure a gidajen kasar da ya kamata su dauki fursunoni dubu 60,899 kacal. 

Wani jami'in wata kungiyar kasa-da-kasa da ke kare hakkin fursunoni a Faransa Prune Missofe, ya ce yanayin da gidajen yarin ke ciki na kara tsananta a kowani wata. 

Ya shawarci gwamnatin kasar "da ta dauki matakan rage cunkoso a gidajen yarin, sannan ta samar da karin wadatattun gine-gine ".

Kotun Kare Hakkin Bil'adama ta Turai a farkon shekarar 2020 ta umarci Faransa ta biya dubban yurayurai ga gomman fursunoni bayan ta gano ba ta daukan matakan rage cunkoson gidajen yarin.

Faransa na sa ran samar da karin gine-ginen a gidajen kasar da za su dauki karin fusunoni dubu15,000 zuwa karshen wa'adin mulkin Emannuel Macron na biyu a shrkarar 2027.

Sai dai kotun wadda ke bincike kan yadda gwamnati ke kashe kudade ta gano a wani rahoton baya-bayan cewa Faransa na tafiyar hawainiya wurin magance matsalar cunkoson gidajen yarin.

Kotun ta ce gwamnatin Faransa ba ta iya gina karin wadatattun dakunan da za su iya daukan fursunoni dubu 7,000 ba a fadin gidajen yarin kasar har zuwa karshen shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.