Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga sun raunata 'yan sanda 108 a Faransa

Akalla ‘yan sanda 108 ne suka samu raunuka tare da kama masu zanga-zanga 291 a fadin Faransa, bayan barkewar rikici a tsakanin su a lokacin zanga-zangar ranar ma’aikata da ke nuna fushin su kan shugaba Emmanuel Macron na garambawul da ya yi wa tsarin fanshon kasar, kamar yadda ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin ya sanar.

Masu zanga-zanga a Faransa.
Masu zanga-zanga a Faransa. © AP - Thibault Camus
Talla

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewar, masu zanga-zangar a birnin Paris sun jefi 'yan sanda tare da fasa gilasan wuraren kasuwanci irin su bankuna da sauran su, lamarin da ya sanya jami'an tsaro yin amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa su. 

Kungiyoyin kwadago sun bukaci jama'ar kasar su fito zanga-zangar ta ranar ma’aikata, don kara sukar tsarin Macron, wanda ke neman kare sauye-sauyen da ya samar. 

Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida ta kasar ta ce kimanin mutane dubu 782 ne suka gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, ciki kuwa har da mutane dubu dari da 12 da suka yi ta su a birnin Paris, duk da cewa kungiyar kwadago ta kasar ta ce adadin ya zarce haka domin a nata alkaluman, mutane miliyan biyu da dubu dari uku ne suka fito don yin zanga-zangar a fadin kasar, ciki kuwa har da mutane dubu dari biyar da 50 da suka gudanar da ta su a babban birnin kasar. 

A watan da ya gabata ne Macron ya rattaba hannu kan dokar da ta kara shekarun yin ritaya daga aiki daga 62 zuwa 64. 

Tun a tsakiyar watan Janairu ne dai ake ta gudanar da yajin aiki da kuma zanga-zanga a kasar akan sauyin da Macron ya yi wa tsarin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.