Isa ga babban shafi

Ukraine ta yi ikirarin samun nasara a kan Rasha a birnin Bakhmut

Ukraine ta yi ikirarin karbe iko da wasu yankuna a birnin Bakhmut inda ake bata-kashi, a yayin da Rasha ta musanta haka, tana mai cewa dakile wani hari ta yi daga dakarun Ukraine.

Shugaban Ukraine,  Volodymyr Zelenskiy.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy. REUTERS - YVES HERMAN
Talla

Rahotannin da bangarorin biyu ke fitowa  na nuni da cewa an samu karuwar rikici a yankin Bakhmut, bayan daa aka samu kwarya-kwaryar kwanciyar hankali na ‘yan watanni.

Yevgeny Prigozhin, wanda shine shugaban kamfanin sojin hayar Wagner, mai jagorancin yakin da ake a Bakhmut ya zargi dakarun Rasha da arcewa daga birnin da ke yaki a  gabashin Ukraine.

Ana cikin rashin tabbas a kan lokaci ko ta inda Ukraine za ta mayar da martini a wannan yaki da ake, dukda cewa a wannan mako shugaba  Volodymyr Zelensky ya ce dakarunsa na bukatar lokacin sake damara.

Fadan baya bayan nan ya barke ne a daidai  lokacin da China ke cewa za ta aike da wani manzo na musamman zuwa Turai a kokarin da take na zama mai shiga tsakani don lalubo zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.