Isa ga babban shafi

Kusan mutum 400,000 gurbatacciyar iska ta kashe a nahiyar Turai - EU

Wani rahoto da Kungiyar Tarayyar Turai ta fitar, ya tabbatar da cewa kusan mutum 400,000 ne suka mutu a nahiyar Turai, sakamakon shakar gurbatacciyar iska.

Yadda hayaki ya mamaye tsaunin Avala na kasar Serbia.
Yadda hayaki ya mamaye tsaunin Avala na kasar Serbia. Getty Images - Djordje Boskovic
Talla

Rahoton, ya nuna cewa wannan ibtila’I ya faru ne a shekarar 2021 kadai, tare da cewar da an bi dokokin da WHO ta gindaya, da addadin basu kai haka ba.

Hukumar kula da muhalli ta Turai, ta ce a tsakanin kasashen Turai kadai, gurbatacciyar iskar da ke shafar mutanen da ke fama da ciwon zuciya, ta yi sanadin mutuwar mutum 253,000 a shekarar 2021 kadai.

Gurbatacciyar iskar da ake samu daga sinadarin nitrogen dioxide ko kuma NO2, ta fi shafar mutanen da ke fama da ciwon sukari, inda ta kashe mutum 52,000

Idan aka hada da kasashen da ke wajen Turai kuwa, EU ta ce, adadin ya kai 389,000 na wadanda suka mutu, sakamakon nau’in iskar nitrogen dioxide NO3

A cewar rahoton, dole ne a dauki matakan kariya, idan har ana son kawo karshen mace-macen mutanen da ke shakar wannan iska mai hadarin gaske, musamman a kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.