Isa ga babban shafi

Wutar daji ta tilasta wa mutane fiye da dubu 30 barin gidajensu a Girka

Wutar Dajin Girka ta ci gaba da tsananta a rana ta 5 bayan tashinta, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da dubu 30 daga tsibirin Rhodes, a dai dai lokacin da masana ke ci gaba da gargadi kan illar dumamar yanayi a bangare guda tsananin zafi ke ci gaba da ta’azzara a kasashen Turai. 

Wutar dajin da ta tashi a kasar Girka tun daga ranar 18 ga watan Yuli.
Wutar dajin da ta tashi a kasar Girka tun daga ranar 18 ga watan Yuli. AFP - VALERIE GACHE
Talla

Girka, Birtaniya Spain da kuma Amurka na sahun yankunan da suka fi fama da matsalar ta wutar daji wadda masana ke alakantawa da dumamar yanayi wadda a shekarun baya-bayan nan ta ke ci gaba da tsananta tare da barazana ga tsirrai da halittun ban kasa  

Wani rahoton kwararru tun gabanin tsanantar wutar dajin ta Girka da ta shiga kwana na 6 a yau Talata ba tare da kakkautawa ba, ya yi gargadin fuskantar tsananin zafi a kasashe daban-daban ciki har da Turai Australia da Arctic baya arewaci da kudancin Amurka. 

A cewar kwararrun tsananin zafin da duniya ke gani ya jefa yiwuwar ceto dazuka daga gobara a hadari fiye da kowanne lokaci a tarihi. 

Baya ga gobarar dajin ta Girka a tsibirin Rhodes da Corfu can a Canada dazuka da dama ke fama da wutar da zuwa yanzu ta kone kadada fiye da dubu 25 kwatankwacin wadda kasashen Chile da Australia suka gani a farkon shekarar nan.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.