Isa ga babban shafi
Gobarar Daji

Gobarar daji ta lakume rayukan mutane 10 a Turkiya da Girka

Gobarar dajin da ta shafe kwanaki tana tafka barna a Turkiya da Girka ta lakume rayukan mutane akalla 10, baya ga fadin kasa mai yawan gaske.

Yadda gobarar daji ke kone kauyen Afidnes, dake arewa da birnin Athens na kasar Girka. 6/8/2021.
Yadda gobarar daji ke kone kauyen Afidnes, dake arewa da birnin Athens na kasar Girka. 6/8/2021. REUTERS - COSTAS BALTAS
Talla

Gobarar ita ce mafi muni da yankunan Girka da Turkiya suka gani cikin gwamman shekaru.

Daruruwan mutane aka kwashe daga yankunan kasashen na Turkiya da Girka bayanda yanayin zafi ya kai digiri 40 zuwa 45 a ma’aunin Celsius.

A Turkiya kadai mutane 8 suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata, yayin da 2 suka mutu a Girka bayan shafe kwanaki akalla 10 ana fama da gobarar dajin.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito, ya bayyana yankin Maditaraniya a matsayin inda tasirin canjin yanayi ya fi muni, tare da gargadin cewa yankin zai fuskanci karin zazzafan yanayi, fari da kuma tashin gobarar dajin a nan gaba, saboda karuwar dumamar yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.