Isa ga babban shafi
Girka - Gobarar Daji

Gobarar daji ta tilastawa daruruwan mutane tserewa daga tsibirin Evia

Daruruwan jami’an kashe gobara a Girka na ci gaba da fafutukar kawo karshen gobarar daji mafi muni da aka gani a kasar cikin gwamman shekaru, wadda kawo yanzu ta kone, dubban gine-gine da gandun daji a tsibirin Evia, abinda ya tilastawa dubban mutane tserewa.

Yadda wutar daji ta kone kauyen Gouves a tsibirin Evia, tsibiri na biyu mafi girma a Girka. 8 ga Agusta, 2021.
Yadda wutar daji ta kone kauyen Gouves a tsibirin Evia, tsibiri na biyu mafi girma a Girka. 8 ga Agusta, 2021. AFP - ANGELOS TZORTZINIS
Talla

Har ila yau, masu aikin agaji sun ce gobarar dajin ta tafka barna a yankin Peloponnese da ke kudu maso yammacin kasar ta Girka, sai dai gobarar da ta tashi a yankin arewacin birnin Athens ta lafa.

Ya zuwa yanzu, mutane biyu suka mutu Girka, takwas kuma makwabciyar ta Turkiyya, inda wasu da dama da suka jikkata ke asibiti.

Yadda gobarar daji ta tunkari wani kauye da ke tsibirin Evia a kasar Girka.
Yadda gobarar daji ta tunkari wani kauye da ke tsibirin Evia a kasar Girka. AP - Petros Karadjias

Girka da Turkiya dai sun shafe kusan makwanni biyu suna fama da mummunar gobarar dajin sakamakon sama da matsanancin zafi da yankunan kasashen biyu ke yi mafi tsanani cikin shekaru da dama.

Bayanai sun ce ruwan sama ya sassauta gobarar dajin da ta tashi a Turkiyya, yayin da kuma a Girka gobarar ke kara karfi sakamakon matsanancin yanayin zafi.

Ma’aikatar bada agajin gaggawar kasar ta Girka ta ce daya daga cikin jiragen saman da ke aikin kokarin kashe gobarar dajin da ke tafka barna ya rikito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.