Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai-Gobarar daji

Tarayyar Turai ta aike da taimako don kashe gobarar daji a Girka, Italiya

Jami’an kashe gobara daga Tarayyar Turai  sun isa kasashen Girka, Italiya, Albania da Arewacin Macedonia da zummar taimakawa wajen kashe gobarar daji da ta addabe su.

Jirgin sama mai saukar ungulu yana kashe gobarar daji a Girka.
Jirgin sama mai saukar ungulu yana kashe gobarar daji a Girka. REUTERS - COSTAS BALTAS
Talla

A wata sanarwa, babbar kwamishinar Tarayyar Turai mai kula da matsaloli da suka shafi bala’o’i,  Janez Lenarcic ta ce suna aiki ba kama hannun yaro wajen aikewa da da taimako, a daidai lokacin da gobarar ke ta’azzara.

Ta jinjina wa kasashen Cyprus, Czech, Faransa, Netherlands da sauran su sakamakon daukar matakin gaggawa ta wajen aikewa da jiragen sama masu kashe gobara da kuma tawagar jami’an kashe gobara don taimaka wa kasashen da gobara daji ta wa illa.

Wannan aikin na aikewa da jiragen sama da jami’an kashe gobara na karkashin jagorancin hukumar kare al’umma ta Tarayyar Turai ne, kuma majalisar gudanarwar Tarayyar Turai ce za ta dauki nauyin akasarin aikin.

Jami’an kashe gobara a kasar Girka na ta kokarin kashe gobarar dajin da ta tashi sakamakon matsanacin zafin da ya kunno kai daga dumamar yanayi, wanda ya lalata gidaje da dama da wuraren sana’o’i, a kewayen birnin Athens, lamarin da ya tilasta kwashe al’ummomin yankin.

Tarayyar Turai ta aike da irin wannan taimako Turkiya a makon da ya gabata don kashe gobarar daji da ta lalata gidajen al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.