Isa ga babban shafi
Wasanni

Wasan Kokuwa ta gargajiya

Wallafawa ranar:

Kokuwa dai na daya daga cikin wasannin gargajiya da ake gudanarwa a kasar Hausa kuma daya daga cikin wasannin da ke nishadantar da al’umma. a cikin shirin na wannan makon zamu ji yadda ake gudanar da wasan na kokuwa inda na kai ziyara daya daga cikin dadalin gudanar da wasan a jahar Lagas Tarayyar Najeriya.

Filin dandalin kokawa a kasar Jamhuriyyar Nijar
Filin dandalin kokawa a kasar Jamhuriyyar Nijar @Niger Official site
Talla

Mutane ne dai dama na iske cike sun kewaye harabar gudanar da wasan kukuwan a dandalin wasan kwaikwayo na Fredom da ke Apapa Jahar lagas, yawancin dai wadanda ke wajen kokuwa matasa ne da ‘yan mata, kodayake akwai masu manya shekaru amma ba kamar yawan matasan ba. Kuma duk karshen mako ne ranakun Assabar ko Lahadi ake gudanar da kokuwar.

Tsarin kokuwar ya shafi yankunan kasashen kasar Hausa, inda Sakkwatawa da katsinawa da kanawa zasu fitar da gwananinsu domin karawa. akan aza kudi duk wanda ya kayar da abokin karawarsa shi zai kwashi kudin da 'yan kallo suka aza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.