El Clasico:hamayya tsakanin Mourinho da Guardiola, Messi da Ronaldo
A gobe Assabar Akwai babbar wasan da zata dauki hankalin duniya A Spain, tsakanin abokan hamayya guda biyu a La liga. Inda Real Madrd zata karbi bakunci Barcelona a Bernabeu, wasan Classico ta farko a bana.
Wallafawa ranar:
Shekaru uku Real Madrid bata lashe kofin La liga ba, amma a bana Madrid ce ke jagorancin Table da maki uku da kuma kwanten wasa tsakaninta da Barcelona, sai Dai Madrid ta san cewa lashe wasanta a karawarta da Barcelona kan iya tabbatar mata da iya lashe La liga a bana, sai dai tsoron Pep Guardiola kocin Barcelona wanda yafi kowane kocin Barcelona samun nasarar madrid a Bernabeu.
A sauran wasannin a La liga Valencia zata kara ne da Real Betis, kuma idan har ta doke Batis zai kasance maki daya ne tsakaninta da Barcelona.
Sevila kuma zata iya gurgusowa matsayi na hudu a saman Table idan har ta doke Lavente.
A ranar lahadi akwai sauran wasannin tsakanin
Rayo Vallecano v Sporting Gijon
Getafe v Granada,
Villarreal da Real Sociedad
Real Zaragoza da Real Mallorca
Malaga da Osasuna
Athletic Bilbao da Racing Santander
Espanyol da Atletico Madrid
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu