Isa ga babban shafi
El Clasico

Barcelona sa’a suka samu inji Mourinho

Mourinho Kocin Real Madrd yace Barcelona sa’a suka samu akan Madrid bayan ya sha kashi hannun ‘Yan wasan Guardiola a filin wasa na Bernabeu ci 3-1.

José Mourinho ya bata fuska bayan ya sha kashi hannun Barcelona ci 3-1.
José Mourinho ya bata fuska bayan ya sha kashi hannun Barcelona ci 3-1. Reuters
Talla

Wannan dai shi ne karo na hudu da Guardiola ke samun nasara lashe wasan Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid a Filin wasa na Bernabeu.

A wasan ranar assabar da aka gudanar, fara wasan ke da wuya cikin dakikoki 22 karim Benzama ya samu sa’ar zirawa madrid kwallo a ragar Barcelona, bayan da mai tsarongidan Barcelona Victor Valdes ya yi kuskuren harba kwallon ga abokan hamayya.

amma kafin zuwa hotun rabin lokaci mintina 30 Alexis Sanchez ya barkewa Barcelona kwallonta, bayan dawowa hutun rabin lokaci ne kuma Barcelona ta samu Karin kwallaye da Xavi da Fabregas suka zira a ragar Madrid.

A wannan karon dai babu zagi babu zargin alkalin wasa amma Mourinho yace Barcelona sa’a ce suka samu musamman kwallon Xavi da ta kauri Marcelo zuwa cikin ragar Madrid.

Yanzu haka a La liga Barcelona ce ke jagorancin Table da yawan kwallaye maki daya tsakaninta da Madrid sai dai kuma Mourinho yana da kwanten wasa daya, inda a karshen mako mai zuwa idan har ya doke Sevilla zai karbi jagorancin Table.

A cewar Mourinho hamayya yanzu aka fara.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.