Isa ga babban shafi
kwallon kafa

Real Madrid da City da Bayern da Juventus sun haska a karshen mako

A wasannin league league da aka gudanar a karshen mako a Nahiyar Turai, Real Madrid ta karbe zagorancin Table hannun Barcelona a La liga bayan ta doke Sevilla ci 6-2. A Ingila kuma Manchester City ce ke ci gaba da jagorancin Table bayan ta doke Arsenal. Juventus kuma ta karbe Jagorancin Table hannun AC Milan.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ke nuna hushinsa ga dan wasan Manchester City Yaya Toure a lokacin da ya sha kashi hannun City ci 1-0 a filin wasa na Etihad a  Manchester
Kocin Arsenal Arsene Wenger ke nuna hushinsa ga dan wasan Manchester City Yaya Toure a lokacin da ya sha kashi hannun City ci 1-0 a filin wasa na Etihad a Manchester REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Ingila

Maki biyu ne ke tsakanin Manchester City da United a saman Table bayan samun nasarar doke Arsenal ci daya mai ban haushi

David Silva ne ya zirawa Manchester city kwallonta a ragar Arsenal bayan dawowa hutun rabin lokaci mintina 53 da fara wasa.

Manchester United kuma ta lallasa QPR ci 2-0 Wayne Rooney ne ya fara zirawa United kwallonata kafin Micheal Carrick ya zira kwallo ta biyu.  Tottenham ce matsayi na uku a saman Table bayan ta doke Sunderland ci daya mai ban haushi. Chelsea kuma ta yi kunnen doki ne ci 1-1 tsakaninta da Wigan, Liverpool kuma ita ce yanzu a matsayi na shida, bayan ta doke Aston villa ci 2-0.

Spain
A Spain kuma Cristiano Ronaldo ne ya zirawa Real Madrid kwallayenta uku inda ta doke Savilla ci 6-2, wannan nasarar ce kuma ya bata damar darewa samar Table maki uku tsakinta da Barcelona.

Dama can, Barcelona ta buga Karin wasa ne domin shiga Gasar Cin Kofin Duniya na Kungiyoyin kwallon kafa kafin buga wasan Classico daya bata damar jagorancin Table bayan ta doke Real Madrid ci 3-1.

Jamus

A Bundesliga kuma, Bayarn Munich ta doke Cologne ci 3-0 duk da cewa a wasan, Alkalin wasa ya daga jan kati ga dan wasan Bayarn Franck Ribery. Yanzu haka kuma maki uku ne ke tsakanin Bayarn Munich da Borussia Dortmund wacce ta doke Freiburg ci 4-1.

Italiya

A Italia kuma Juventus ta dawo shugabancin Table bayan ta doke Novara ci 2-0, Inter Milan kuma, sai ci gaba da farfadowa take yi inda ta samu takowa zuwa matsayi na biyar bayan ta doke Cesena ci 1-0.

A ranar Assabar AC Milan ta dan ji kamshin jagorancin Table bayan ta doke Siena ci 2-0 kafin Juve ta buga wasanta.

Udinese kuma ta koma matsayi na uku bayan a tashi wasanta ci 2-2 tsakaninta da Lazio.

A farkon kakar wasa dai Inter ta fuskanci kalubale inda take can kasan Table ajin ‘yan baya. Amma ko yanzu akwai sauran aiki a gare ta domin maki 10 ne tsakaninta da Juventus da ke jagorancin Table.

Faransa

A Faransa wasa tsakanin PSG da Lille an tashi ne babu ci.

Sakamakon wasan ne kuma ya hanawa PSG samun yawan makin jagorancin Table tsakaninta da Montpellier wacce ita ma ta yi kunnen doki ci 1-1 tsakaninta da Toulouse.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.